Burkina Faso ta kori wasu jami'an diflomasiyyar Faransa uku
Gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso ta kori wasu jami'an diflomasiyyar Faransa guda uku, bisa zarginsu da yiwa kasar zagon kasa.
Wallafawa ranar:
Jami'an diflomasiyyar da suka hada da masu ba da shawara kan harkokin siyasa biyu, an ba su wa'adin sa'o'i 48 da su fice daga kasar, duk da cewa gwamnatin bata bayyana takamaiman abubuwan da take zargin su a kai ba, illa zagon kasa.
Wannan matakin ya kara dagula dangantaka tsakanin Burkina Faso da Faransa tun bayan da sojoji suka karbi mulkin kasar a shekarar 2022.
A baya dai gwamnatin mulkin sojin ta kori sojojin Faransa, tare da sallamar jakadan Faransa da ke kasar, inda kuma ta dakatar da wasu kafafen yada labaran kasar da ta yi mata mulkin mallaka a baya.
Rahotanni daga kasar dai na cewa, sallamar Faransawan na da nasaba ne da zaman tattaunawar da suka yi da wasu kungiyoyin fararen hula.
Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta fuskanci suka kan yadda take murkushe ‘yancin fadin albarkacin baki, a daidai lokacin da ake fuskantar kalubalen tsaro daga kungiyoyin ‘yan ta’adda masu alaka da Al Qaeda da IS.
Tuni dai ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta yi watsi da zargin da ake musu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu