Isa ga babban shafi
Sudan ta kudu

Ana jin karar harbe-harbe a Juba babban birnin kasar Sudan ta Kudu

Rahotanni daga Sudan ta Kudu na cewa ana jin karar harbe harben bindigogi a Juba tun wayewar safiyar yau lahadi gabanin soma shagulgulan cikar kasar shekara biyar da samun ‘yancin kai.

Sojojin Sudan ta kudu a Juba babban birnin kasar
Sojojin Sudan ta kudu a Juba babban birnin kasar REUTERS
Talla

Sama da dakaru 150 ne suka rasa rayukansu a cikin wani fada da ya barke a ranar juma’a tsakanin dakarun gwamnatin kasar Sudan ta kudu da na bangaren ‘yan tawaye a Juba babban birnin kasar.

Wannan na zuwa ne a yayin da kasar ke shirin soma shagulgulan cikar shekara 5 da samun yancin kai.

Yakin basasa na sama da shekaru biyu ya matukar daidaita wannan jinjirar kasar inda aka samu asarar dubban rayukan mutane baya ga miliyoyi da suka tsere daga mahallinsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.