Isa ga babban shafi
Ethiopia- South Sudan

'Yan Bindiga Daga Sudan Ta Kudu Sun Kashe Fararen Hula 140 a Kasar Habasha

Jami'an kasar Habasha sun ce wasu ‘yan bindiga daga kasar Sudan ta Kudu sun kai wani kazamin samame wani gari dake kan iyakan kasashen nasu, inda suka kashe fararen hula 140 sannan suka kwashi ganima.

Fira Ministan Habasha Hailemariam Desalegn da Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da kuma Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya a wata ganawa a shekara ta 2013.
Fira Ministan Habasha Hailemariam Desalegn da Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da kuma Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya a wata ganawa a shekara ta 2013. 照片来源:路透社REUTERS/Hakim George
Talla

Kasar Habasha ta ce an kai samamen ne shekaranjiya Juma'a, a kan iyaka inda ita Habasha ke kula da ‘yan gudun hijira samada dubu 284 da suka gujewa yaki da ake fafatawa a Sudan ta Kudu.

Acewar wata sanarwa daga Gwamnatin Habasha,  sojan ta sun fatattaki ayarin ‘yan bindigan har an kashe 60 daga ciki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.