Isa ga babban shafi

Jam'iyun adawa a Togo sun bukaci ECOWAS ta soke gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar.

Gamayyar jam’iyyun adawa a Togo sun shigar da kara gaban kotun ECOWAS, suna rokon da ta soke gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar.Jam’iyyun dai sun yi zargin cewa gyaran fusakar da aka yi wa kundin zai kange su daga samun damar darewa karagar mulki, tare da bawa shugaba Faure Gnassingbe damar ci gaba da kasancewa akan karagar.

hoton daya daga cikin 'yan adawar siyasar Togo
hoton daya daga cikin 'yan adawar siyasar Togo AFP - PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Rikicin siyasa a kasar ta Togo dai na ci gaba da karuwa tun bayan da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.

A watan da ya gabata ne mahukuntan kasar suka amince da yin gyara a kudin, gabanin zaben ‘yan majalisar dokokin kasar na 29 ga watan da muke ciki na Afrilu.

Sabon kudin dai da aka kwaskware ya mayar da kasar zuwa kan tsarin Firaminista maimakon tsarin shugaban kasa da ta ke kai a baya.

Sai dai gamayyar jam’iyyun adawar kasar sun yi tsaiwar gwamen jaki kan cewa bazata sabu ba, dalilin ma da ya sanya su shigar da kara gaban kotun ta ECOWAS.

A cikin kunshin takardar korafin mai dauke da sa hannu jam’iyyun adawar kasar 13 da wasu kungiyoyin fararen hula, sun bukaci kotun da ta hukunta gwamnatin bisa take dimokaradiyya, tare kuma da yin fatali da gyararren daftarin kundin tsarin mulkin kasar.

A baya dai mahukunta a kasar sun haramtawa jam’iyyun adawar gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar.

Masu suka dai na kallon wannan sauyi a matsayin sabon matakin da Gnassingbe ya dauka, na tsawaita wa'adin mulkin da Iyalan gidansu suka shafe tsawon lokaci suna yi.

Tun a shekarar 2005 ne Sojojin kasar suka nada shi don ya gaji mahaifinsa da ya rasu, wanda ya shafe kusan shekaru 40 yana mulki kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.