Isa ga babban shafi

Togo ta koma tsarin fira minista bayan sauya kundin dokokinta

A jiya Juma’a ne ƴan majalisar dokokin Togo suka kada ƙuri'a a karo na biyu, inda suka amince da gyaran da suka yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar, wanda ya sauya fasalin ƙasar daga wacce ta ke a turbar shugaba mai cikakken iko da al’umma ke zaba, zuwa shugaban da ƴan majalisar dokoki ke zaba.

Taswirar ƙasar Togo
Taswirar ƙasar Togo © Studio FMM
Talla

Wannan mataki dai na zuwa ne kwanaki 10 gabanin gudanar da zaben ƴan majalisar dokokin ƙasar da za a gudanar.

Tun a ranar 25 ga watan da ya gabata ne majalisar dokokin Togo ta amince da sabon kundin tsarin mulkin ƙasar, sai dai shugaba Faure Gnassingbe ya bukaci ƴan majalisar su sake bitar sa, bayan bayyana shi da ƴan adawa suka yi a matsayin juyin Mulki.

Jam’iyun adawa dai na ganin gyaran fuskar da aka yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar a matsayin wani yunkuri na tsawaita shugabancin shugaba Gnassingbe, da ya ɗare kujerar shugabancin ƙasar tun a shekarar 2005, bayan da ya gaji mahaifinsa da ya jagoranci kasar na kusan shekaru 40.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.