Isa ga babban shafi

Yan Sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a jamhuriyar Benin

A Jamhuriyar Benin,'Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa a yau Asabar don tarwatsa zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa da kungiyoyin kwadago suka shirya a cibiyar tattalin arzikin  wannan kasa wato Cotonou.Rahotanni daga birnin na nuni cewa an hango wasu gungun masu zanga-zangar na kokarin sake taruwa kafin ‘yan Sanda su sake tarwatsa su ta hanyar harba hayaki mai sa hawaye.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Jamhuriyar Benin
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Jamhuriyar Benin AFP - ABADJAYE JUSTIN SODOGANDJI
Talla

Babbar Kungiyar Kwadago ta kasar wato (CSA Benin), ta yi nuni da cewa 'yan sanda sun kama shugabanta Anselme Amoussou.

Ma'akata da 'yan kasuwa na ci gaba da kokawa ganin halin tsadar rayuwa da jama'a suka shiga,kazzalika rufe kan iyaka tsakanin kasar ta Benin da Jamhuriyar Nijar ya saka jama'a cikin wanin halin damuwa.

Tashar jiragen ruwan birnin Kwatanu
Tashar jiragen ruwan birnin Kwatanu © Prosper Dagnitche / AFP

A cewar wata majiyar kungiyar, an kama masu zanga-zangar guda goma sha biyu a dai dai lokacin da wasu yan kasar ke sa ran samun karin haske daga rundunar ‘yan sandan wace ta yi shuru a kan wannan kame .

Birnin Cotonou a kasar Benin
Birnin Cotonou a kasar Benin AFP - YANICK FOLLY

'yan siyasa bangaren adawa na zarin shugaban kasar Patrice Talon da kasancewa dan kama kariya,wanda ya soke duk wasu dokoki da suka jibanci hakkin dan Adam a kasar ta Benin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.