Isa ga babban shafi

Wasu kasashen yammaccin Afirka sun daura damarar yaki da cutar cizon sauro

Kasashen Benin da Liberia da kuma Saliyo sun kaddamar da wani shiri na yaki da cutar zazzabin cizon sauro, karkashin wani shiri mai taken Africa-focussed initiative da zummar ceto rayuwar dumbin kananan yara da ke mutuwa kowacce shekara a Nahiyar Afirka.

Cutar Zika na yaduwa ne ta hanyar cizon sauro da sumbata da kuma jima'i
Cutar Zika na yaduwa ne ta hanyar cizon sauro da sumbata da kuma jima'i REUTERS/Jaime Saldarriaga
Talla

Kungiyar GAVI da ke taimakawa wajen samar da ingatatun riga kafin yaki da cututtuka, ta bayyana cewa kasashen uku na yankin yammacin Afirka  sune na baya-bayannan da suka shiga tsarin tun bayan da aka kaddamar da shirin na riga kafin yaki da cutar cizon sauro ga kananan yara, a kasashen Burkin Faso da Kamaru da Ghana da kuma Malawi.

GAVI ta ce shirin da hukumar lafiya ta duniya ta amince da shi na da zummar  aiki tare raba gidan sauro don magance cutar ta zazzabin cizon sauro, wadda a Afirka ke kasha kananan yara ‘yan kasa da shekaru 5 a kowacce shekara.

Yayin da babbar jami’ar shirye-shiryen Kungiyar ta GAVI Aurielia Nguyen ta bayyana cewa bullo da wannan zai taimakawa iyalai da dama wajen ceto kananan yara har da manyansu daga kamuwa da balahirar cutar da sauro ke yadawa .

A yayin kaddamar da shirin dai kungiyar ta ce Benin ta samu magungunan riga kafin dubu dari 215,900, sai Saliyo da ta samu dubu dari 550,000, Liberia kuma ta samu dubu dari 112,000,  wadda za a yiwa  yara ‘yan kasa da shekaru 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.