Isa ga babban shafi

EU ta koka game da yadda aka hana jami'anta sanya idanu a zaben Chadi

Kungiyar Tarayyar Turai, ta yi tir da Allah wadai da yadda mahukuntan kasar Chadi suka hana masu sanya idanu kan zaben kasar kusan dubu 3 gudanar da aikin su yadda ya dace.

Har yanzu ana jiran sakamakon zabe
Har yanzu ana jiran sakamakon zabe AFP - ISSOUF SANOGO
Talla

Mafi yawan masu sanya idanun da aka hana gudanar da aiki yadda ya dace na cikin tawagar da EU din ta dauki nauyi.

Tuni dai yan adawa suka bukaci a kauracewa zaben a cewar su an tafka manyan kura kurai da kuma tafka magudi.

Suma dai kungiyoyin da suka shiga kasar don sanya idanu game da zaben sun ayyana shi a matsayin wanda ke cike da kura-kurai ganin yadda gwamnati ta gaza yin komai da ya shafi zaben a bayyane.

Har yanzu dai ana dakon sakamakon zabe, wanda bashi da wani armashi kasancewar ‘yan adawa basu yi wani karsashi a zaben ba.

To sai dai hakan bai zo da mamaki ba, kasancewar dama an yi hasashen hakan tun kafin zuwa zabe, la’akari da yadda gwamnatin rikon kwarya ta rika murkushe ‘yan adawa ta hanyar hana su tsayawa takara da sauran su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.