Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane sama da 70 a kenya tare da raba wasu da dama daga matsugunansu

Gwamantin Kasar Kenya ta bayyana cewa dadin mutanen da suka mutu a ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu bayan na damina a watan Maris ya kai 70, yayin da kusan rabin wadanda suka mutu a birnin Nairobi.

Ambaliyar ruwa a Kasar Kenya
Ambaliyar ruwa a Kasar Kenya © Monicah Mwangi / REUTERS
Talla

Kasar Kenya da wasu kasashe a gabashin Afirka yankin da ke fama da matsalar sauyin yanayi ya sha fama da mamakon ruwan sama a 'yan makonnin nan, tare da kakkarfar iskar El Nino.

El Nino wani yanayi ne wanda ke da alaka da tsanantar zafi da ake fuskanta, wanda ke haifar da fari a wasu sassan duniya.

Kakakin gwamnatin kasar Isaac Mwaura ya bayyana cewa, kididdigar jami'an 'yan kasar Kenya wadanda suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan ya kai mutane 70,kamar yadda kakakin gwamnatin kasar Isaac Mwaura ya wallafa bayanin a shafinsa na X, bayan da mamakon ruwan sama ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da goma a Nairobi babban birnin kasar cikin makon nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.