Isa ga babban shafi

Janyewar dakarun Najeriya a yankin Allawa ya sanya al'uma tserewa

Rundunar sojin Najeriya ta rufe sansaninta tare da janye dakarunta da ke yankin Allawa na yankin karamar hukumar Shiroro a jihar Nejan kasar.

Dakarun sojin Najeriya.
Dakarun sojin Najeriya. YouTube
Talla

Yankin na Allawa dai na daya daga cikin yankunan da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a wannan karamar hukmar ta Shiroro. Wadda dalilin janye dakarun ya haifar da da dawowar fuskantar farmaki akai akai a yankin da makoftansu.

Hakazalika janyewar dakarun ya haddasa jama’a da dama tserewa daga matsugunansu wanda ya kunshi mata da dattawa da kuma kananan yara wadda ke tattaki na tsawon kilomita akalla 50 kafin su samu isa wuri mafi dacewa da kwanciyar hankali.

Yayin da wasu daga cikin mazauna yankin da su bukaci a sakaya sunansu suka bayyanawa jaridar Daily Trust cewa su dai sun wayi gari kawai a ranar alhamis 25 ga watan Afrilu, suka ga sojojin na ciccire kayayyakinsu a kokarin da suke yi na barin yankin.   

Indai ba a mance ba a ranar Talata, 23 ga watan Afrilun 2024 ne sojojin suka wani  abu da ya fashe a hanayarsu tashiga garin na Alllawa, sai dai babu  wanda ya mutu amma wasu da dama sun jikkata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.