Chadi ta kaddamar da bincike kan Kebzabo
Hukumomin Kasar Chadi sun yiwa shugaban ‘yan adawar kasar Saleh Kebzabo tambayoyi saboda zargin da ya yi na batar wasu sojojin Gwamnati 20, kwana guda bayan rantsar da shugaba Idris Deby wa’adi na biyar.
Wallafawa ranar:
Ma’aikatar shari’ar kasar tace ta kadadmar da bincike kan shugaban Yan adawar kamar yadda mai gabatar da kara ya bukata.
Ranar 28 ga watan Afrilu, kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch da Amnesty International sun yi zargin cewar sama da sojojin gwamnati 20 da wasu jami’an tsaro suka bata bayan sun ki yarda su goyi bayan takarar shugaba Idris Deby.
Kungiyoyin tare da gwamnatin Faransa sun bukaci gudanar da bincike akai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu