Isa ga babban shafi
Jamus

Jamus ta soki kasashen dake kin baki musulmi

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta soki wasu kasashen Turai da suka ki karbar baki musulmi bisa dalilai na tsaro, Merkel ta bukaci magance matsalar ta’addanci maimakon juyawa bakin dake cikin halin kunci baya.

Angela Merkel da shugaban Turkiya a sansanin 'Yan gudun hijra dake Gaziantep
Angela Merkel da shugaban Turkiya a sansanin 'Yan gudun hijra dake Gaziantep 路透社
Talla

Kasashen Turai kamar su Czech da Poland da Hungary da kuma Slovakia ne suka yi watsi da tsarin kungiyar Tarrayar Turai na rarraba dubban bakin hauren dake jibge a sansanonin ‘yan gudun hijra dake Turkiya da Girka bayan tserewa rikice rikicen yaki a kasashensu.

Kasar Jamus tace tana saran baki dake neman mafaka 300,000 zasu isa kasar a cikin wannan shekara, wanda shine kashi daya bisa uku na wadanda suka isa kasar bara.

Jamus ta bakin Shugaban Ofishin kula da baki da kuma Yan gudun hijira Frank-Jurgen Weise yace habakar tattalin arzikin kasar zai bada dama wajen karbar bakin ba tare da matsala ba.

Jami’in yace a hukumance suna saran karbar baki 250,000 zuwa 300,000 duk da matsalar da suka samu na hare hare.

Bara kawai baki miliyan daya da dubu dari daya suka isa kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.