Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe ya koma gida daga jinya a Dubai

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya koma kasar tasu yau Asabar daga Dubai inda wasu bayanai ke cewa rashin lafiya ta kai shi Daular Larabawa.

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe
Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe Reuters/Philimon Bulawayo
Talla

Mugabe mai shekaru 92 ya kasance shugaba mafi tsufa a kujeran mulki a kasashen Africa.

Cikin raha ya shaidawa manema labarai cikin harshen Shona a filin jiragen sama na Zimbabwe a lokacin da ya sauka cewa 'na mutu ne na dawo kamar yadda na saba'.

Rashin koshin lafiyar shugaban dai ya zama abin da ake ta zantuka a fadin kasar, amma kuma akoda yaushe ya kan ce shi tamkar yau aka haife shi yake ji.

Yanzu haka dai Hukumomin kasar na ta fafutukan yadda zasu biya albashin soja, ‘yan sanda da sauran maaikatan kasar ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.