Jama'ar Sudan ta Kudu sun bukaci tura karin dakarun wanzar da zaman lafiya
Jama’a da ke gudun hijira da kuma jagororin addini a Suda ta Kudu, sun yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta gaggauta tura Karin dakarun da ta yi niyyar yi zuwa kasar, saboda mawuyacin halin da mutane ke ciki.
Wallafawa ranar:
Kiran ya zo ne yayinda gwamnatin Sudan ta Kudun, ke cigaba nuna rashin amincewa bisa tura mata Karin dakarun wanzar da zaman lafiya 4000, inda ta bayyana hakan a matsayin wani yanayi na yunkurin mamaye kasar.
Wani limamin Katolika a kasar, Ark bishop Paulino Lukudu ya ce dole ne Sudan ta Kudun ta bukaci Karin dakarun Majalisar Dinkin Duniyar, domin dawo da zaman lafiya a kasar.
A satin da ya gabata rundunar sojin Sudan ta Kudu ta sanar da cewa ta gurfanar da wasu jami'anta 60 da aka zarga da aikata laifukan yaki, da suka kunshi sata, kisan kai, da kuma azabtar da mutane.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu