Somalia ta karbi bakuncin taron Shugabanni karo na farko tun 1991
Ranar Talata kasar Somalia ta karbi bakuncin gudanar da taro na wasu daga cikin shugabannin kasashen Afrika a birnin Mogadishu, karo na farko tun bayan barkewar rikici a kasar a shekarar 1991.
Wallafawa ranar:
Taron ya maida hankali ne kan yadda za’a gudanar da zaben shugaban kasa dana ‘yan majalisu a kasar, sai kuma tattaunawa kan halin da kasar Sudan ta Kudu ta ke ciki.
Kasashen da suka halarci taron sun hada da Kenya, Habasha, Uganda, Djibouti, da kuma Sudan.
Kasashen dai sun cimma matsayar hada kai domin murkushe tada kayar bayan kungiyar Al-Shabaab a Somalia, da kuma farfado tattalin arzikin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu