Isa ga babban shafi
Somalia

Al Shebab ta kashe mutane a harin Mogadishu

Akalla mutane bakawi ne suka rasa rayukansu sakamakon harin kunar bakin wake da kungiyar Al Shebab da kaddamar a sansanin sojin kasashen Afrika da ke birnin Mogadishu na Somalia.

Mutane bakwai sun mutu a harin da kungiyar Al Shebab ta kaddamar a sansanin sojin kasashen Afrika da ke birnin Mogadishu na Somalia
Mutane bakwai sun mutu a harin da kungiyar Al Shebab ta kaddamar a sansanin sojin kasashen Afrika da ke birnin Mogadishu na Somalia REUTERS/Feisal Omar
Talla

Rahotanni sun ce, fashewar bama-baman ta tarwatsa tagogin filin jiragen sama da ke kusa da birnin, inda gilasan tagogin suka war-watsu kan fasinjojin da suka iso birnin a safiyar yau.

Jami’an ‘yan sanda sun ce, maharin farko ya tarwatsa motar da yake dauke da ita cike da bama-bamai, yayin da mahari na biyu ya yi kokarin kutsawa tsakiyar sansanin na sojin da ke aikin wanzar da zaman lafiya.

Sai dai maharin na biyu bai samu nasarar kutsawa ciki ba, inda bam dinsa ya tarwatse bayan jami’an tsaro sun harbe shi da bindiga a kofar shiga sansanin.

A cikin wata sanarwa da ta fitar bayan kaddamar da harin, kungiyar ta Al Shebaba ta ce, mutane 12 ta hallaka a harin na yau Talata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.