Isa ga babban shafi
kenya

An kashe 'yan sandan Kenya a ofishinsu

Wani mutum da ake zargin yana da alaka da kungiyar al Shebab ya harbe ‘yan sandan Kenya guda hudu har lahira bayan ya yi nasarar fisge bindiga daga hannun wani jami’in tsaro.

Wani mutun ya kashe 'yan sandan Kenya bayan ya kwace bindiga daga hannun wani jami'in tsaro a Kenya
Wani mutun ya kashe 'yan sandan Kenya bayan ya kwace bindiga daga hannun wani jami'in tsaro a Kenya REUTERS/Siegfried Modola
Talla

Lamarin ya auku ne a ofishin ‘yan sanda da ke yankin Kapenguria kusa da iyakar Uganda da Kenya inda ake tsare da mutumin saboda zargin da ake yi masa na sanya matasa cikin kungiyar al Shebab ta Somalia mai ikirarin jihadi.

Rahotanni sun ce a safiyar yau ne mutumin ya kwace bindigar daga hannun jami’in tsaron da ke gadin ofishin ‘yan sandan, inda nan take ya dirka wa mutune hudu daga cikin su harsashai.

A jiya laraba ne aka kama shi domin fuskanatar tuhuma kan laifin da ake zarginsa da aikatawa amma ya aikata wannan danyan aikin kamar yadda majiyar ‘yan sanda ta ce.

A halin yanzu, dan bindigar ya garkame kansa a wani daki yayin da jami’an tsaro ke kokarin samar da dabarun kutsawa domin damke shi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.