Isa ga babban shafi
Faransa-Afrika-Jamus-Turai

Sake dawo da martabar Turai a siyasance

Faransa da Jamus na kokarin ganin sun sake dawo da martabar kungiyar tarrayar Turai,hakan dai na zuwa ne bayan da Francois Hollande Shugaban Faransa yayi wata ganawa da waziriyar Jamus Angela Markel a yau alhamis a fadar l'Elysée dake birnin Paris.

Shugaban Faransa Francois Hollande da waziriyar Jamus Angela Merkel
Shugaban Faransa Francois Hollande da waziriyar Jamus Angela Merkel REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Shugabanin biyu sun yi kira ga takwarorinsu na kasashen turai 27 da ke shirin gudanar da taro a gobe juma’a a Bratislava domin samar da ingantacen tsari na kungiyar tarayyar turai da ya tsinci kansa cikin mawuyacin hali sakamakon ficewar Britaniya daga cikin kungiyar.
Kasashen turai za su futar da wani sabon tsari na sake dawo da martabar Turai a Duniya don magance matsallolin dake gaf da mamaye yankin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.