Kotu ta tabbatar da nasarar shugaba Ali Bongo
Kotun fasalta kundin tsarin mulkin kasar Gabon, ta tabbatar da nasarar shugaba Ali Bongo Ondimba, a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar, bayan tayi watsi da bukatar ‘yan adawa na a sake kirga kuri’un da aka kada yayin gudanar da zaben.
Wallafawa ranar:
A gefe guda kuma yayin da al’umar kasar ta Gabon ke zaman zulumi kan fargabar barkewar rikici, gwamnatin kasar ta ce zata dora alhakin duk wani tashin hankali da ya auku, kan jagoran ‘yan adawa Jean Ping.
Tuni dai aka baza ‘yan sandan kwantar da tarzoma, a sassan titunan kasar cikin shirin ko ta kwana.
A baya magoya bayan jagoran 'yan adawa Jean Ping sun zargi kotun da yunkurin yi musu rashin adalci yayin yanke hukunci kan karar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu