Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

An tarwatsa dalibai a Afrika ta Kudu

'Yan sanda a Afrika ta Kudu na amfani da karfi da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa gungun dalibai da ke zanga-zanga a Johannesburg kan karin kudin makaranta.

Wasu daga cikin dalinam jami'ar Wit a lokacin wani gangami a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu
Wasu daga cikin dalinam jami'ar Wit a lokacin wani gangami a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu
Talla

Arangamar tsakanin dalibai da jami’an tsaro ta biyo bayan kokarin da hukumomin kasar suka yi na sake bude jami’ar Wits da aka rufe tsawon makonni biyu saboda zanga-zangar daliban.

Jami’ar Wits da sauran jami’o’in kasar na rufe tsawon lokaci sakamakon gangamin da daliban ke yi kan karin kudin makaranta, in da mafi yawan gangamin ke rikidewa zuwa arangama da jami’an tsaro.

Hukumomin jami’ar Wits sun sha alwashin sake bude makarantun a yau Talata, in da shugaban jami’ar Adam Habib ke gargadin rashin kammala kakar karatun bana.

Rahotanni sun ce, an ta amfani da harsassan roba da hayaki mai sa kwalla wajen tarwatsa gungun daliban da suka yi kokarin hana bude jami’ar ta Wits.

Batun adawa da karin kudin makaranta a Afrika ta Kudu na sake ta’azzara, yayin da gwamantin kasar ke nuna cewa ba za ta janye kudurinta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.