Isa ga babban shafi
Africa ta Kudu

Dubban masu zanga-zanga a Afrika ta kudu sun bukaci Zuma ya yi murabus

 A yau laraba ne dubban al’ummar kasar Africa ta Kudu suka gudanar da zanga-zanga, inda suka bukaci shugaban kasar Jacob Zuma da ya gaggauta yin murabus daga mukaminsa don ceto tattalin arzikin kasar daga durkushewa.

Masu zanga-zanga a birnin Pretoria
Masu zanga-zanga a birnin Pretoria REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

A zanga zangar ta yau laraba da aka gudanar a manyan biranen kasar kamar su Capetown da Pretoria an yi ta ganin da dama daga cikin dubban masu zanga zangar dauke da allunan dake cewa Jacob Zuma ka kasa akwai kuma wanda ke cewa Zuma ka yi murabus.

Rudanin dai ya biyo bayan wasu sauye sauye na mukamin ministan kudi da shugaba Jacob Zuma ya yi ta yi, inda da farko Zuma ya sauya Nhlanhla Nene da David Van Rooyen kwatsama bayan kwanaki hudu da nada Van Rooyen ministan kudin shugaba Zuma ya sake korar sabon ministan inda ya maye gurbin sa da Pravin Gordhan.

A wannan dan tsakanin da Zuma yake ta kwan gaba kwan baya ne tattalin arzikin kasar ta Africa ta kudu ya tabarbare ganin faduwar kudin kasar wato rand a kasuwanin duniya.

Wannan ya kara tabbatar da zargin cin hanci da kuma rigingimu a jam’iyar ANC da shugaban ya gagara magancewa ga kuma batun cewa jam’iyar na gab da rasa tagwamnashinta musanman ganin yadda ake hasashen cewa da kyar zata sha a zaben kanana hukumomi da ake shirin yi a shekara mai zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.