Isa ga babban shafi
Kenya

Kwamishinonin hukumar zaben kasar Kenya sun yi murabus

Daukacin Kwamishinonin hukumar zaben kasar Kenya sun sauka daga mukaman su bayan an kwashe watanni a na zanga zanga a kasar saboda rashin amincewa da matsayin na su.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta TONY KARUMBA / AFP
Talla

Babban hafsa a fadar shugaban kasar, Joseph Kinyua, ya ce kwamishinonin 10 sun mika takardun su na murabus, kuma yanzu haka ta na kokarin ganin an maye gurbin su da wasu wadan da za su gudanar da zaben shekara mai zuwa.

'Yan adawa a karkashin tsohon Firaminista Raila Odinga sun zargi kwamishinonin ne da goyan bayan gwamnatin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.