Isa ga babban shafi
Najeriya

Alkalai : Muna yaki ne da rashawa inji Buhari

Fadar shugaban Najeriya ta ce samamen ‘Yan sandan farin kaya ta kai tare da kama wasu manyan alkalan kasar, an yi hakan ne domin fada da rashawa amma ba akan bangaren shari’a na kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS
Talla

Sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu ya fitar ta bayyana cewa an kai samamen a karkashin tsari na doka, kuma fadar shugaban ta samu tabbaci daga hukumar ‘yan sandan farin kaya da ke cewa akwai sammacin da ya bayar da damar yin hakan.

Kungiyar lauyoyin Najeriya ta bakin shugabanta Abubakar Mahmoud ta yi kakkausar suka da wannan matakin, yayin da ita kuma jam’iyyar adawa ta PDP ta ce kama alkalan abu ne da ya sabawa doka, tana mai cewa an yi garkuwa ne da su.

Amma a sanarwar da Garba Shehu ya fitar ya ce Shugaba Buhari Mutum ne da ke mutunta tsarin dimokuradiya da kundin tsarin mulki.

Hukumar DSS dai ta ce Jami’anta sun kwato makudan kudade a gidajen Alkalan da suka yi wa dirar mikiya a daren Juma’a zuwa wayewar safiyar Asabar a jihohin kasar 6 da kuma Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.