Isa ga babban shafi
CAF

CAF ta takaita wa’adin shugabanta

Hukumar kwallon kafar Afrika CAF ta takaita wa’adin shekarun shugabanta zuwa shekaru 12 kamar yadda ta tabbtaar a yau Litinin. Tsarin shugabancin hukumar zai kasance na shekaru 4 a wa’adin shugabanci uku, kuma tsarin zai soma aiki daga badi.

Issa Hayatou, Shugaban hukumar kwallon Afrika
Issa Hayatou, Shugaban hukumar kwallon Afrika FABRICE COFFRINI / AFP
Talla

A can baya dai babu wani wa’adin shugabanci a tsarin CAF inda tun a 1998 Issa Hayatou ke jagorantar hukumar har zuwa yanzu.

Hayatou ya shafe shekaru 28 yana jagorantar hukumar kwallon kada ta Afrika

Kuma Hayatou ya nuna alamun zai tsaya takarar shugabancin hukumar a karkashin sabon tsarin kamar yadda ya shaidawa RFI.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.