Isa ga babban shafi
ICC

ICC ta sami Bemba da aikata laifi a Congo

Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ta ce ta sami tsohon mataimakin shugaban Jamhuriyar Demokradiyar Congo kuma jagoran ‘yan tawaye Jean Pierre Bemba da laifin bai wa shedu cin hanci don kare shi a tuhumar da kotun ke masa na aikata laifukan yaki a rikicin kasar da ya hallaka daruruwan mutane.

Jean-Pierre Bemba
Jean-Pierre Bemba REUTERS/Michael Kooren
Talla

Akwai makusantar Bemba hudu da Kotun ta zartas musu da hukunci bisa rawar da suka taka don bayar da shedar karya bayan sun karbi cin hanci daga hannun Bemba.

Kotun ta tattaro bayanai da suka kunshi nadar muryoyi da wasu sakwanni ta waya da kuma takardun banki da Bemba ya tura wa mutanen da aka kama da laifin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.