Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari zai tattauna da Majalisa kan cin bashi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai ci gaba da tautaunawa da ‘Yan Majalisar Dattawan kasar da suka ki amincewa da bukatar ciyoo bashin Dala miliyan 30 da gwamnatin shi ke son gudanar wasu manyan ayyuka.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki a Masallacin Idi
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki a Masallacin Idi thebreakingtimes.com
Talla

Sanata Ali Ndume ya ce Majalisar ta bukaci cikakken bayani kan ayyukan da za a yi da kudin ne kafin amincewa da shi.

Mai taimakawa shugaba Buhari kan harkokin Majalisa, Ita Enang ya ce za su gabatarwa Majalisar da bayanan da suke bukata domin ganin sun sauya matsayinsu.

Sai dai wasu na kallon matakin da Majalisar ta dauka a matsayin siyasa, sakamakon takun-sakar da ake samu tsakanin bangaren zartarwa da Majalisa.

Gwamnatin Buhari dai na fuskantar suka da matsin lamba akan tafiyar hawainiyar da ake yi ga kokarin magance matsalar tattalin arzikin da Najeriya ta shiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.