Isa ga babban shafi
Gambia

Jammeh ya gabatar da takardun takara a Gambia

Shugaban Gamabia Yahya Jammeh ya gabatar da takardunsa na sake tsayawa takara don neman wa’adi na biyar a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a cikin watan Disamba mai zuwa.

Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh
Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

A jiya Alhamis ne Jammeh mai shekaru 51 ya mika takardun ga hukumar zaben kasar tare da shaida wa shugaban hukumar cewa, ko kadan bai damu da kalaman da mutane ke yi a kansa ba.

Tun bayan juyin mulkin shekarar 1994, shugaba Jammeh ya dare kan karaga, yayin da wasu ke kallon sa a matsayin mai mulkin kama-karya.

A bangare guda, Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Gwamnatin Gambia da ta saki fursunonin siyasar da ta ke tsare da su kafin gudanar da zaben.

Wakilin Sakatare Janar na Majalisar a Afrika ta Yamma, Mohammed Ibn Chambas ya bukaci sakin mutane 30 da aka kama a lokacin zanga-zangar da aka yi a watan Afrilu da kuma wasu 14 da suka bukaci sauya dokokin zaben kasar.

Chambas ya kuma bukaci bai wa ‘yan siyasar kasar damar gudanar da harkokinsu ba tare da tsangwama ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.