Isa ga babban shafi
Mozambique

Gobarar tankar mai ta kashe mutane 73 a Mozambique

Mutane fiye da 70 ne suka rasa rayukansu bayan wata tankar mai ta kama da wuta a kudancin kasar Mozambique.

Mutane fiye da saba'in ne suka mutu a gobarar tankar mai a Mozambique
Mutane fiye da saba'in ne suka mutu a gobarar tankar mai a Mozambique
Talla

A sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar, ta ce tankar ta kama da wuta ne a yayin da jama’a ke rige-rigen dibar man fetur daga tankar da ta lalace a kauyen kafin daga bisani ta kama da wuta inda mutane fiye da saba’in suka rasa rayukansu.

Hukumomin kasar sun ce hadarin ya yi muni sosai ganin yadda mutane suka kone kurmus wasu da dama kuma suka sami munanan rauni.

Yanzu haka jami’an aikin agaji sun bazama don taimakawa mutanen da suka ji rauni a hadarin na yau.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.