Isa ga babban shafi
Gambia

ECOWAS za ta yi taro a Najeriya kan Gambia

Shugabannin Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma za su gudanar da wani taro a ranar Asabar a Najeriya don tattaunawa kan halin da ake ciki a Gambia.

Shugaban Gambian Yahya Jammeh da shugabannin kungiyar kasashen ECOWAS da suka hada da Muhammadu Buhari na Najeriya da Ellen Johnson Sirlef na Liberia da John Mahama na Ghana
Shugaban Gambian Yahya Jammeh da shugabannin kungiyar kasashen ECOWAS da suka hada da Muhammadu Buhari na Najeriya da Ellen Johnson Sirlef na Liberia da John Mahama na Ghana Nigeria president Twitter account
Talla

Wannan na zuwa ne bayan ganawar da tawagar shugabanin ta yi da shugaba Yahya Jammeh da zababben shugaban Gambia Adama Barrow da nufin shawo kan Jammeh don ganin ya mika mulki ga Barrow cikin sauki.

Shugabar kungiyar ECOWAS Ellen Johnson Sirleaf ta ce, babu wata yarjejeniya da aka kulla a ziyar tasu duk da kyayawa tarbar da suka samu.

Shugaban gudanarwar kungiyar Marcel de Souza ya ce, idan tattaunawa ta gagara, makwabtan Gambia na iya tunanin amfani da karfi don kawar da Jammeh daga mulki.

Shugaba Jammeh wanda ya jagoranci Gambia na tsawon shekaru 22 ya ki amince wa da shan kayi a zaben da aka gudanar a ranar 1 ga watan Disamaba bayan ya zargi jami’an hukumar zaben kasar da tafka kura-kurai.

Tuni dai jam’iyyarsa ta fara shirin shigar da kara a kotu don kalubatantan sakamakon, wanda Jammeh ya amince da shi da farko kafin daga bisani ya bijire.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.