Isa ga babban shafi
Somalia

Harin kunar bakin wake a Somalia

A Somalia mutane 18 ne suka mutu bayan da wata mota shake da bama-bamai ta tarwatse,wannan dai ne karo na farko tun bayan hawan karagar mulkin kasar  daga Shugaban kasa Mohamed Abdullahi Mohamed. 

Harin yan kungiyar Al Shebab a Somalia
Harin yan kungiyar Al Shebab a Somalia REUTERS/Feisal Omar
Talla

Harin na yau lahadi ya haifar da rudani cikin  babban birnin kasar Mogadiscio,ya yinda yan Sanda ke ci gaba da gudanar  da bincike domin gano kungiyar dake da alhakin  kai wannan kazamin hari.

Somalia da jimawa ,hukumomin kasar tareda hadin guiwar  kasashen Duniya na kokarin kawo karshen rashin kwanciar hankali da wasu kungiyoyi dauke da makamai  da suka hada da yan Al Shebab ke ci gaba da kai wa tareda kisan dubban jama'a .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.