Isa ga babban shafi
Somalia

Somalia: An toshe manyan hanyoyi a Mogadishu kafin zabe

Hukumomin Somalia sun haramta zirga-zirgar ababen hawa tare da toshe manyan hanyoyin a Mogadishu babban birnin kasar, saboda zaben shugaban kasa da za a gudanar a gobe Laraba.

Gwamnatin Somalia ta haramta zirga-zirga a Mogadishu
Gwamnatin Somalia ta haramta zirga-zirga a Mogadishu REUTERS
Talla

Rahotanni sun ce a kafa mutane ke tafiya inda za su, saboda barazanar tsaro daga mayakan Al Shebaab masu alaka da al Qaeda.

A gobe Laraba ne ‘Yan Majalisa za su jefa kuri’ar zaben sabon shugaban kasa tsakanin ‘Yan takara 23 da suka hada da shugaban kasar mai ci Hassan Shiekh Mahamud.

Tun a watan Agusta ya kamata a gudanar da zaben bayan shugaban kabilun kasar sun zabi ‘Yan Majalisa wadanda kuma ke da alhakin zaben shugaban kasa.

Somalia da ta fada cikin tashin hankali tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Siad Bare a shekarar 1991.

Yanzu haka an dauki tsauraran matakan tsaro domi ganin an gudanar da zaben ba tare da samun tashin hankali ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.