Isa ga babban shafi
Najeriya

An sako Jamusawa da aka sace a Kaduna

A Najeriya Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da sakin wasu yan kasar Jamus biyu da aka sace makon jiya.Jamusawan masu bincike ne na abubuwan tarihi da ke karkashin kasa, wadanda suka ziyarci kauyen Jajela da ke karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna. 

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i
Talla

Sanarwar da mai Magana da yawun Gwamna na Jihar Samuel Aruwan ya raba, ta ce Gwamna Nasir El Rufai ya yabawa jami’an tsaro wajen ceto Jamusawan biyu.
An dai sace Jamusawan ne makon jiya, bayan kashe wasu ‘yan Najeriya biyu dake tare da su a wani kauye da suke gudanar da bincike.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.