Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Dalibai a Sudan ta Kudu sun ki halartar zana jarrabawa

Daruruwan Dalibai a kasar Sudan ta kudu sun kasa samun damar gudanar da jarabawar kamala makaranta saboda yadda suka ki bin umurnin gwamnati na ficewa daga sansanin yan gudun hijirar Majalisar Dinkin Duniya dan zuwa inda za’ayi jarabawar.

Wata karamar yarinya da ta tserewa fada a Sudan ta Kudu, a sansanin 'yan gudun hijira na Bidi Bidi da ke arewacin Uganda.
Wata karamar yarinya da ta tserewa fada a Sudan ta Kudu, a sansanin 'yan gudun hijira na Bidi Bidi da ke arewacin Uganda. REUTERS/James Akena/File Photo
Talla

Hakan ya faru ne saboda fargabar rashin tsaro da ake fama da shi a kasar.

Hukumomin kasar sun ce akalla dalibai 900 matsalar ta shafa a Juba, kuma matakin zai shafi damar da suke da ita ta zuwa jami’a.

Akasarin wadannan dalibai dai tun shekarar 203 suke zama a sansanin sakamakon barkewar sabon fada tsakanin yan kabilar Dinka ta shugaba Salva Kiir da Nuer ta shugaban yan tawaye Riek Machar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.