Isa ga babban shafi
Najeriya

Dalilin rashin ganin Buhari a bainar Jama’a

Fadar Shugaban Najeriya ta yi karin haske dangane da rashin ganin shugaba Muhammadu Buhari a bainar jama’a, inda ta ce babu wani abin fargaba dangane da halin da ya ke ciki.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari venturesafrica
Talla

Mai taimakawa shugaban ta hanyar yada labarai, Garba Shehu ya ce rashin halartar Buhari taron Majalisar ministoci ranar laraba wani mataki ne da ya zo a karshen lokaci, dalilin ya sa ba a sanarwa jama’a da wuri ba ke nan.

Shehu ya ce likitocin shugaban sun ba shi shawarar ya yi taka-tsantsan wajen gudanar da ayyukansa kuma matakin da ya ke bi ke nan.

Fadar shugaban ta ce duk da halin da Buhari ke ciki ana tafiyar da ayyukan gwamnati ba tare da matsala ba, kuma mataimakinsa Yemi Osibanjo na ganawa da shi akai akai don yi ma sa bayani.

Tun bayan dawowarsa daga jinya a kasar Ingila a ranar 10 ga watan maris da ya gabata, shugaban Muhammadu Buhari ya rage fitowa bainar jama’a ko kuma halartar taruka.

Har yanzu batun rashin lafiyar shugaban na ci gaba da janyo cece kuce a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.