An ceto bakin haure 484 daga cikin teku
Jami’an tsaron gabar ruwan Italia sun ce sun ceto baki 484 dake cikin wasu kananan kwale kwale a tekun Mediterenian a karshen makon da ya gabata, cikin su harda gawawaki 7.
Wallafawa ranar:
Kungiyar dake sa ido kan mutanen dake kaura ta ce a cikin wannan shekara kawai baki 45,000 suka isa Italia ta cikin kwale kwale daga Arewacin Afirka, wanda ke nuna cewar an samu Karin kashi 40 kan bakin da aka samu bara.
Masu tsaron gabar ruwan dai basu bayyana kasashen da bakin suka fito ba, amma kuma akasarin baki daga yammacin Afirka da Bangladesh ne ke bi ta kasar Libya dan isa nahiyar Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu