Isa ga babban shafi
Chadi

Rashin lafiyar Buhari ya kawo cikas ga yaki da Boko Haram- Deby

Shugaban Chadi Idris Deby, ya ce rashin kasancewar shugaba Muhammadu Buhari a cikin Najeriya, abu ne da ya kawo cikas ga ayyukan rundunar hadin-gwiwa da ke yaki da ayyukan Boko Haram.

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou, da na Benin Thomas Boni Yayi, da na Chadi Idriss Deby da kuma na Najeriya Muhammadu Buhari a tattaunawar da suka yi a Abuja kan yaki da Boko Haram a Abuja, watan Yunin 2015.
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou, da na Benin Thomas Boni Yayi, da na Chadi Idriss Deby da kuma na Najeriya Muhammadu Buhari a tattaunawar da suka yi a Abuja kan yaki da Boko Haram a Abuja, watan Yunin 2015. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Deby, wanda ke zantawa da wasu kafafen yada labaran Faransa ciki har da Rfi a fadarsa a Ndjamena, ya ce tun daga lokacin da Buhari ya fara fama da rashin lafiya babu wani babu tsayayyen Jami’i daga Najeriya da suke magana da shi.

An tambayi Deby ko yana ganin an samu nasara a kan kungiyar Boko Haram ? sai shugaban ya ce, "tabbas an yi nasara akan kungiyar, amma sakamakon rashin lafiyar shugaba Muhammadu Buhari, watanni hudu ke nan ba mu da wani tsayayyen mutum da muke tattaunawa da shi dangane da batun na Boko Haram a Najeriya".

A cikin zantawar, shugaba Deby ya yi barazanar janye dakarun kasarsa daga wasu ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasashe da dama na Afirka saboda rashin kudi.

Shugaba Idris, ya ce janye dakarun daga wasu ayyukan wanzar da zaman lafiya ya zama wajibi, lura da irin makudan kudaden da ake bukata domin daukar dawainiyarsu, yayin da kasar ta Chadi ke fama da matsaloli musamman na tattalin a cikin gida.

Deby, ya bayyana matukar bacin ransa a game da yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ki amincewa ta dauki nauyin rundunar da kasashen yankin Sahel 5 ke shirin kafawa domin yaki da ayyukan ta’addanci a yankin.

Shugaban ya ce Chadi ba za ta iya ci gaba da bai wa Majalisar Dinkin Duniya gudunmuwar dakaru 1400 a Mali ba sannan a lokaci guda ta bayar da wasu dakarun 2,000 ga rundunar G5 ta Sahel.

Shugaban ya bayar da misali da irin rawar da Chadi ke takawa don yaki da ayyukan ta’addancin Boko Haram a kasashen Najeriya, Nijar da kuma Kamaru, yayin da kuma kasar ke kokarin kare iyakarta mai tsawon kilomita 1.200 da Libya.

Kungiyar Boko Haram dai na ci gaba da yin barazana a Najeriya da kuma makwabta.

A watan jiya ne shugaba Buhari ya tafi London domin sake diba lafiyarsa, bayan shafe watanni biyu ba ya Najeriya a tafiyarsa ta farko a watan Janairu.

Har yanzu dai ‘yan Najeriya ba su san irin rashin lafiyar da ke damun shugabansu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.