Isa ga babban shafi
Nijar

Boko Haram: Sojojin Nijar sun kashe masunta 14 bisa kuskure

Sojojin Jamhuriyyar Nijar sun kashe wasu masunta 14, wadanda aka bude wa wuta bisa zaton cewa ‘yan Boko Haram ne a lokacin da suke kamun kifi a yankin Jihar Diffa da ke kan iyaka da Najeriya.

Yankin Diffa na cikin dokar ta baci a Nijar domin yaki da Boko Haram
Yankin Diffa na cikin dokar ta baci a Nijar domin yaki da Boko Haram ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Bayanai sun ce 12 daga cikin mutanen da aka kashe ‘yan gudun hijira ne da suka tsere wa rikicin Boko Haram daga garin Abadan da ke cikin Najeriya, yayin da sauran biyun ‘yan Nijar ne da ke rayuwa a wani wuri da ke gaf da kan iyakar Nijar da Najeriya.

Yankin Diffa dai na cikin dokar ta-baci, inda aka hana kamun kifi da mafi yawanci mutanen yankin ke dogaro a matsayin sana’a. Kuma Abadan yanki ne da aka hana yawo inda duk wanda aka gani a daji za a dauke shi matsayin dan Boko Haram.

Rahotanni sun ce mutanen sun ruga da gudu ne a lokacin da suka tsinkayi jami’an tsaro.

Boukar Mani Orthe, magajin garin Toumour, wanda a cikin yankinsa ne lamarin ya faru, ya ce mutane sun saba fita zuwa bakin Kogi domin kamun kifi kuma sojoji sun kai farmaki ne bayan sun samu rahoton da ya danganta mutanen a matsayin ‘Yan Boko Haram.

Yankin Diffa dai na ci gaba da fama da hare haren ‘Yan Boko Haram inda ko a makon jiya mayakan sun shiga kauyen Ngalewa suka sace yara 37 tare yi wa wasu 9 yankan rago.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.