Al'ummar Rwanda na bikin nasarar Kagame
Al’ummar Rwanda na gudanar da bikin murnar nasarar da shugaba Paul Kagame ya samu a zaben shugabancin kasar karo na uku, in da ya yi alkawarin ci gaba da kawo sauyi a kasar.
Wallafawa ranar:
Shugaba Kagame da ya fara jagorantar Rwanda tun bayan kawo karshen kisan kare dangi a shekarar 1994, ya samu sama da kashi 98 cikin 100 na kuri’un da aka kada.
Sai dai ana zargin shugaban da yin mulkin kama-karya, amma mutanen kasar na yaba ma sa saboda rawar da ya taka wajen inganta tattalin arzikinsu.
Kimanin mutane miliyan 6 da dubu 900 ne suka fito don kada kuri’unsu, yayin da Kagame mai shekaru 59 ya shafe tsawon shekaru 17 akan karagar mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu