Isa ga babban shafi
Sahel

Kwamitin tsaro ya tsayar da ranar kai ziyara yankin Sahel

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai aike da wata tawaga zuwa kasashen yankin Sahel da suka hada da Mali da Burkina Faso da kuma Mauritania domin tattaunawa da mahukuntan kasashen dangane da rundunar da ake shirin kafawa da za ta yi fada da ayyukan ta’addanci a yankin.

Ministan harakokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian  a wata ziyara da ya kai a Niamey Nijar
Ministan harakokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian a wata ziyara da ya kai a Niamey Nijar RFI/Olivier Fourt
Talla

Daga ranar 19 zuwa 23 ga wannan wata na Oktoba ne tawagar za ta ziyarci kasashen, a daidai lokacin da bayanai ke cewa an shirya tsaf domin ganin cewa rundunar da ake kira G5-Sahel ta fara ayyukanta gadan-gandan.

Jakadan Faransa a Majalisar Dinkin Duniya François Delattre wanda ake kyautata zaton zai kasance a cikin tawagar, ya ce batun kudaden tafiyarwa shi ne babban kalubale da rundunar ke fuskanta a yanzu, kuma wannan ziyara za ta kara bai wa kasashen duniya haske dangane da muhimmancin kafa rundunar.

G5-Sahel wadda tuni ta samar da dakaru dubu biyar, sun fito ne daga kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da kuma Nijar, sai dai daga cikin kudade Euro milyan 223 da ake bukata don daukar dawainiyarta, duka duka Euro milyan 108 ne suka shiga hannu.

Babbar manufar kafa rundunar dai ita ce yaki da ayyukan ta’addanci da masu fataucin miyagun kwayoyi da kuma makamai a wannan yanki an Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.