Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Martanin kasashen Duniya dangane da abinda ke faruwa a Zimbabwe

Kungiyoyi da sauran kasashe Duniya na cigaba da mayar da martani game da yunkurin sojoji na karbe mulki a kasar Zimbabwe.A nata martanin Tarayyar turai ta yi kira da a warware matsalar cikin lumana domin kaucewa abinda zai haifar da rikici a kasar.

Robert Mugabe,wanda sojoji ke tsare da shi yanzu haka
Robert Mugabe,wanda sojoji ke tsare da shi yanzu haka REUTERS/Rogan Ward
Talla

Kungiyar Turai ta yi kira ga duk wadanda al’amarin ya shafa da su koma teburin shawara domin warware al’amarin cikin lumana.

Kungiyar ta ce tana lura da yadda al’amura ke gudana a kasar, inda ta jaddada cewa akwai bukatar a martaba hakkokin fararen hula, sannan a martaba kundin tsarin mulki .

A nata bangaren, kasar Birtaniya ta bukaci da a kaucewa duk abinda zai haifar da zubar da jini a Zimbabwe.

Sakataren harkokin kasashen waje na Burtaniya Boris Johnson, ya ce yanzu haka ba za a iya hasashen abinda zai faru a kasar ta Zimbabwe ba, amma dai abu mafi muhimmanci shi ne kowa na son ya ga an samu zaman lafiya a kasar.

Tuni dai mai rikon mukamin jakadar Burtaniya a kasar ta Zimbabwe Simon Thomas ya bukaci ‘yan kasar sa da ke zaune a Zimbabwe da su zauna a gidajensu.

A na shi bangaren, shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya ce a zantawarsu ta waya, Mugabe ya shaida masa cewa yana tsare ne a gida, sannan ya ce kasar ta Afirka ta Kudu za ta aike da manzanni na musamman zuwa kasar.

A cikin sanarwar da kasar ta Afirka ta kudu ta fitar ta bayyana cewa za ta aika da tawaga wacce ta kunshi ministan tsaro da kuma tattara bayanan sirri na kasar.

A nashi bangaren, shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya bukaci da a zauna lafiya sannan kuma a mutunta doka a kasar ta Zimbabwe.

A cikin sanarwar da shugaban kasar ya fitar ta hannun mai ba shi shawara a harakokin yadda labarai Femi Adesina, Shugaba Buhari ya bukaci dukkanin bangarori a kasar su guji abubuwan da za su kawo tashin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.