Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP ta tsawaita wa'adi ga masu son tsayawa takara

Jam’iyyar PDP da ke adawa a Najeriya, ta tsawaita wa’adin da ta bai wa wadanda ke son tsayawa takarar wasu mukamai a babban taronta domin sayen fom daga 19 har zuwa 30 ga wannan watan nuwamba.

Tutar jama'iyar PDP mai mulki a Najeriya
Tutar jama'iyar PDP mai mulki a Najeriya PDP-website
Talla

Kwamitin da aka dora wa alhakin shirya babban taron zaben sabbin shugabanni, ya ce ya yanke shawarar tsawaita wa’adin ne lura da yadda ake samun karuwar jama’a da ke neman tsayawa takarar mukamai.

 

Wannan ne dai karo na farko da jam’iyyar ke shirin zaben sabbin shugabanni tun bayan gudanar da zaben shugabancin kasa a Najeriya inda PDP ta sha kaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.