Isa ga babban shafi
Mali

Toumani Toure tsohon Shugaban Mali zai koma gida

Tsohon shugaban Mali Amadou Toumani Toure da ke gudun hijira a Senegal tun 2012, zai koma kasar nan zuwa karshen wannan mako, a wata sanarwa da fadar Shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita.

Tsohon shugaban Mali Amadou Toumani Toure
Tsohon shugaban Mali Amadou Toumani Toure
Talla

Idan aka yi tuni hambararren Shugaban kasar Mali Amadou Toumani Toure ya yi murabus daga mukamin shi na shugaban kasa karkashin yarjejeniyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS domin kawo karshen rikicin kasar bayan Sojoji sun kifar da gwamnatinsa.

Yarjejeniyar kuma ta amince da dage takunkumin da aka kakabawa kasar Mali tare da yin afuwa ga Sojojin da suka hambarar da gwamnatin Toure.

Hambararren shugaban kasar, Amadou Toumani Toure ya fito a kafar talabijen ta kasar Faransa inda ya ce yarjejeniyar kungiyar ECOWAS, mataki ne mai kyau ga ci gaban Mali.

Karkashin yarjejeniyar dai, kakakin majalisar kasar Dioncounda Traore, aka daurawa alhakin jagorantar gwamnatin rikon kwarya domin gudanar da zabe nan da kwana 40.

Wasu mukarraban hambararren shugaban sun ce ATT zai dawo gida ne bayan da ya samu tabbaci daga shugaban kasar mai ci Ibrahim Boubacar Keita cewa za a kare mutuncinsa idan ya dawo gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.