Isa ga babban shafi
Najeriya

Za a siyawa Buhari takaddar takara a 2019

Wata kungiyar matasan Daura da ake kira Daura Emirate Youth Progressive Movement a Jihar Katsina da ke tarayyar Najeriya, ta sha alwashin siyawa shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari takaddar samun damar tsayawa takara zagaye na biyu yayin babban zaben kasar na 2019.

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari na ci gaba da shan suka musamman dangane da salon kamun ludayinsa na tsuke bakin aljihu wanda ya jefa mutane da dama cikin matsanancin talauci baya ga tashin farashin kayakin masarufi.
Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari na ci gaba da shan suka musamman dangane da salon kamun ludayinsa na tsuke bakin aljihu wanda ya jefa mutane da dama cikin matsanancin talauci baya ga tashin farashin kayakin masarufi. Nigeria Presidency/Handout via Reuters
Talla

Yayin wani gangamin da dubban matasan suka gudanar a garin na Daura don nuna goyon baya ga Muhammadu Buhari, shugaban kungiyar Malam Abdulkadir Lawal, ya ce ba su da gudunmawar da za su sakawa shugaban da shi face saya masa takaddar takarar la’akari da yadda ya ke hidimtawa ‘yan kasar.

A cewar Abdulkadir Lawal, Shugaba Buhari ya taka rawar gani wajen bunkasa yankin nasu, musamman a al’amuran da suka shafi tsaro da harkokin noma baya ga samar da guraben ayyukan yi.

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari na ci gaba da shan suka musamman dangane da salon kamun ludayinsa na tsuke bakin aljihu wanda ya jefa mutane da dama cikin matsanancin talauci baya ga tashin farashin kayakin masarufi.

Sai dai kuma a bangare guda wasu na jinjinawa shugaban kan nasarar da ya yi a bangaren yaki da ayyukan ta’addancin kungiyar Boko Haram dama fatattakar rashawa baya ga baza komar tattalin arziki tare da dawo da martabar kasar a idon Duniya.

Ko da yake dai wasu na ganin akwai bukatar shugaban ya koma gefe don bayar da dama ga matasa su tafiyar da kasar, yayinda wasu ke ganin har yanzu akwai bukatar ya dora don aiwatar da wasu gyare-gyare.

Har yanzu dai babu wasu bayanai a hukumance da ke nuna shugaban zai sake tsayawa.

Sai kalaman da ke fitowa baya-bayan nan na tabbatar da cewa akwai yiwuwar shugaban ya sake tsayawa takarar a zaben shekarar 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.