Libya
Harin masallacin Benghazi ya jikkata kusan mutane 100
Wasu hare-haren Bom da tsakar ranar yau a masallacin juma'a da ke birnin Benghazi na Libya ya hallaka mutum guda, yayinda ya jikkata kusan mutane 100.Rahotanni sun ce harin shi ne irinsa na farko a baya-bayan nan da aka kai wurin ibada.
Wallafawa ranar:
Talla
Jami’an tsaro sun ce bom na farko an boye shi ne cikin masallacin yayinda na biyu kuma a waje ajiye takalma.
Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin, amma sai dai ya jefa garin cikin rudani.
Ko a ranar 24 ga watan Junairu ma an kai makamancin wannan hari a kan masallatan tare da hallaka kusan mutane 50.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu