Gabashin Libya ta haramtawa Amurkawa zuwa kasar
Gwamnatin da ke iko da Gabashin Libya ta haramtawa Amurkawa zuwa kasar a wani matakin na mayar da martani kan umurnin shugaba Donald Trump na hana ‘yan Libya zuwa Amurka.
Wallafawa ranar:
Gwamnatin da ke karkashin Abdullah al-Thinni tare da kwamandan soji Khalifa Haftar ta bayyana cewar abin takaici ne yadda Amurka ta sanya sunan Libya cikin jerin kasashen da ta hana mutanen su zuwa Amurka.
Al-Thinni ya ce matakin Amurka bai dace ba la'akari da yadda sojojin kasar suka tashi tsaye suna yaki da ayyukan ta’addanci.
Libya na daga cikin kasashe 8 da Amurka ta bayyana a matsayin wadanda aka haramtawa jama’ar su zuwa Amurkan saboda tsaro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu