Ramaphosa ya yi wa Majalisar Ministocinsa garambawul
Sabon shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya yi wa Majalisar Ministocin kasar garambawul kwanaki 11 bayan hawarsa karagar mulki, in da ya mayar da Nhlanhla Nene wanda Jacob Zuma ya kora a matsayin Ministan Kudi.
Wallafawa ranar:
Shugaban ya kuma nada David Mabuza, Firimiyan Yankin Mpumalanga a matsayin mataimakin shugaban kasa, tare da wasu sabbin mukaman ministoci da mataimakansu 30.
Rahotanni sun ce, shugaban ya kori wasu daga cikin ministocin Zuma, yayin da ya nada tsohuwar matarsa, Nkosaza Dlamini-Zuma da suka fafata da ita wajen neman shugabancin Jam’iyyar ANC a matsayin ministar tsare-tsare a fadar shugaban kasa.
Mr. Ramaphosa ya dare kan kujerar shugabancin kasar ne bayan jam'iyyar ANC ta kori Zuma bisa zargin cin hanci da rashawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu