Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Takaitaccen tarihin Cyril Ramaphosa sabon shugaban Africa ta kudu

Sabon shugaban wanda asalin sunansa shi ne, Matamela Cyril Ramaphosa an haife shi ranar 17 ga watan Nuwamban 1952 a garin Soweto na Africa ta kudu, ya yi karatu a matakin Firamare da Sakandire a garin na Soweto kafin daga bisani ya tafi matakin babbar kwaleji a Sibasa Venda ya kuma yi karatun jami’a Turfloop inda ya karanta fannin alkalanci.

Sabon shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa.
Sabon shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa. REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Tun yana makaranta Ramaphosa na jagorantar kungiyoyin dalibai musamman masu adawa da nuna kyamar bakaken fata, dalilin da ya sa a lokuta da dama ake daure shi tsawon watanni.

Bayan gogewar da ya samu a fannin shugabanci da gwagwarmaya kwatar ‘yanci, tun yana da karancin shekaru, Ramaphosa ya zamo fitaccen dan kasuwa yayinda ya tsunduma harkokin siyasar kasar a shekarar 1982.

Sabon shugaban wanda ke da jarin kasuwanci na fiye da dalar Amurka miliyan 450, ya jagoranci kafa kungiyar kwadago inda ya shugabance ta tsawon lokaci haka zalika mamba ne har yanzu a kungiyar da ke fafutukar yaki da nuna wariya, haka kuma ya jagoranci wata kungiya ta daban da ke fafutukar kare hakkin dan adam.

Sabon shugaban yanzu shi ne shugaban kasa na biyar a Afrika ta kudun wadda ta samu ‘yan ci a shekarar 1934, kuma ya taka gagarumar rawa wajen ganin an gudanar da sahihin zaben kasar a shekarar 1994.

Rahotanni sun ce tun kafin yanzu Ramaphosa shi ne zabin Jagoran gwagawarmaya kuma tsohon shugaban kasar Nelson Mandela inda a lokuta da dama ya nuna bukatar ganin an tsayar da shi takarar shugabancin kasa.

Ramaphosa na daga cikin na gaba-gaba da suka matsa kaimi ga shugaba Jacob Zuma don ganin ya sauka daga karagar mulki tun bayan zarge-zargen da suka fito da akewa Zuman kan cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.