Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Ramaphosa ya zama sabon shugaban Afrika ta Kudu

Majalisar Dokokin Afrika ta Kudu ta zabi Cyril Ramaphosa a matsayin sabon shugaban kasar bayan Jacob Zuma ya yi murabus sakamakon matsin lambar da ya sha daga jam’iyyrsa ta ANC saboda zargin cin hanci da rashawa.

Sabon shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa
Sabon shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa REUTERS/Rogan Ward
Talla

A jawabinsa na farko bayan nada shi, Ramaphosa, ya lashi takobin yaki da cin hanci da rashawa, yayin da ake kallon kalamansa tamkar shagube ga tsohon shugaban kasar, Jacob Zuma.

A yayin jawabi a gaban Majalisar Dokokin Kasar, Ramaphosa ya bayyana wasu tarin matsaloli da ya ce suna addabar kasar.

Daga cikin matsalolin akwai batun cin hanci da rashawa da durkushewar harkokin kasuwanci da kuma yadda wasu kamfanoni mau zaman kansu suka yi kane-kane a harkokin gwamnati.

Ramahosa ya ce, wadannan sune matsalolin da sabuwar gwamnatinsa za ta tinkara.

A jiya ne daiu Mr. Zuma ya yi murabus tare da fadin cewa, ba zai amince a zubar da jinin wani ba saboda shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.