Isa ga babban shafi
Kamaru

Paul Biya ya bai wa jami'an tsaro umurnin murkushe 'yan aware

Shugaban Kamaru Paul Biya, ya lashi takobin ci gaba da  daukar matakin soji don murkushe ‘yan awaren da ke yankin masu  amfani da Turancin Ingilishi.

Shugaban Kamaru Paul Biya lokacin da ya kai ziyara a fadare Elyseea Paris, Janairun 2013.
Shugaban Kamaru Paul Biya lokacin da ya kai ziyara a fadare Elyseea Paris, Janairun 2013. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Biya ya bayyana aniyarsa ce a yayin  jagorantar  taron Majalisar Zartaswar kasar na farko da ya jagoranta a jiya Alhamis bayan ya shafe kimanin shekaru biyu ba tare da ya halarci irin wannan taro na mako-mako ba.

A cewar shugaba Biya, daukar matakin soji ne abin da ya fi dacewa da ‘yan awaren matukar ana son dawo da al’amura yadda ya kamata a yankin.

A ranar daya ga watan Oktobam 2017 ne ‘yan awaren suka shelanta kafa kasarsu mai suna Ambazonia, daga kasar Kamaru, yankin da ke da kaso biyar na jama’ar kasar.

Yanzu haka dai shugaba Paul Biya ya bai wa dakarun kasar  umarnin kutsawa yankin na ‘yan awaren, cikin shirin yaki, tare da jirage masu saukar ungulu da tankokin yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.