Isa ga babban shafi
Somalia

Al Shebab ta yi ikrarin kashe dakarun wanzar da zaman lafiya na Afrika 59

A Somaliya kungiyar al Shebab ta bayyana kashe dakarun sojan samar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika Amisom da na gwamnatin Somaliya 59 a wasu jerin hare haren da suka kaddamar kan rundunar a yankin Bas-Shabelle, dake kudancin Magadisho babban birnin kasar.

zanen taswirar kasar Somaliya
zanen taswirar kasar Somaliya Google Maps
Talla

Al Shabab ta bayyana cewa ta kai hare-hare rabin dozin, ta ce ta kashe sojojin kungiyar tarayyar Afrika 59 mafiya yawansu kuma sojojin kasar Uganda ne, a yayin da su kuma suka ce an kashe masu rasa mayaka 14.

Daga nasu bangaren Dakarun Uganda sun bayyana mutuwar sojojinsu 4 ne, ba kamar yadda al Shebab ta sanar ba, a yayin da su ka ce sun kashe mayakan na Shebab 22.

Mafi yawan hare haren dai, an kai su ne ta hanyar harba rokoki kan sansanonin sojin samar da zaman lafiyar na Amisom dake da sansani a yankin na Bas-Shabelle.

An dai kai harin na jiya Lahadi da aka kai a wani waje mai tazarar kilo mita 130 kudu maso yammacin Mogadiscio, kan sansanin Bulomarer ya kazance.

A cewar wani mejon sojan Somaliya Farah Osman, wasu yan kunar bakin wake 2 ne a cikin motoci suka fara tarwatsa kansu da bama bamai a kan ayarin motocin dakarun wanzar da zaman lafiyar na tarayyar Afrika da kuma kasar ta Somaliya.

Kafin mayakan al Shebab dake boye su shiga buda wuta, daga bisani kuma suka kutsa kai a cikin sansanin dakarun na Afrika. Fadan da Mejo Farah Osman ya bayyana a matsayin kazamin fada tsakanin bangarorin biyu.

Ana dai ganin hare haren na al Shebaba kan rundunar kokarin wanzar da zaman lafiya a Bulomarer a matsayin maida martani kan harin marecen ranar assabar da ta gabata da dakarun na Afrika tare da hadin guiwar sojan somaliya suka kai ne kan a wasu kauyuka dake yankin ne.

Yankin Bas-Shabelle dai, ya na kasancewa daya daga cikin yankunan da kungiyar al Shebab ke ci gaba da cin karenta babu babbaka a kasar ta Somaliya duk kuwa da muhimmancin da yake dashi ta fannin tsaro lura da makwabtakar da yake yi da birnin Mogadisho.

Duk kuwa da dakaru dubu 22 da take da su da kuma kusancin Bas-Shabelle da Mogadisho rundunar kokarin wanzar da zaman lafiyar ta tarayyar Afrika Amisom ta kasa wajen rab ayan taáddan na al Shebab da yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.